Posts

Showing posts from August, 2018

Na fi duk wani kocin firimiya — Mourinho

Image
Na fi duk wani kocin firimiya — MourinhoKocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ya fi duka masu horas da kungiyoyin gasar firimiya a halin yanzu, "don sau uku ina lashe kofunan gasar," a cewarsa.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan rashin nasarar da kungiyarsa ta yi a gida a hannun Tottenham a ranar Litinin.

A taron da ya yi da manema labarai bayan wasan, kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya fusata.

Da yake magana kan shan kayen da Man U ta yi a Old Trafford, Mourinho ya ce idan mutane sun san ma'anar kwallaye ukun da aka sha Man United, to za su san cewa shi ya fi sauran masu kula da kungiyoyin gasar Firimiya.

Mourinho ya ce, hakan ya faru ne domin shi ya ci gasar Firimiya sau uku yayin da duka sauran takwarorinsa na gasar firimiya a yanzu sun ci gasar ne sau biyu kacal jumulla.

Sai dai dan wasan gaban Tottenham, Harry Kane, ya ce nasarar da kungiyarsa ta samu a kan Man U a Old Trafford sun isar da wani babban sako.

A wata hira da ya y…