Posts

Showing posts from October, 2018

Rikicin Kaduna: Buhari ya fusata, ya sanar da matakin da zai dauka

Rikicin Kaduna: Buhari ya fusata, ya sanar da matakin da zai dauka

A yau Lahadi ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da sanarwar saka dokar ta baci tare da hana 
mutane fita na tsawon sa'o'i 24 a kwaryar birnin Kaduna da kewaye domin dakile yaduwar tarzomar da ta tashi a garin.
A daren yau ne shugaba Buhari ya yi alla-wadai da rikicin na jihar Kaduna da ya yi sanadiyar asarar rayukan mutane 55 tare da bayyana cewar ba zai taba yarda da wofantar da ran bil'adama da zubar da jini ba. Buhari ya ce babu wani addini da ya yarda da tashin hankali. A sakon da shugaban ya fitar a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewar tilas ya yi tofin ala-tsine a kan rikicin da ya yi sanadin rasa rayuka 55. Shugaba Buhai ya bayyan cewar ya bawa rundunar 'yan sanda damar daukan dukkan matakin da zai kai ga dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a garin Kaduna. Kazalika ya bayyana cewar ya umarci shugaban rundunar 'yan sanda ya tura runduna ta musamman tare da sanar da shi halin da ake ciki a k…

Ankashe Mutane Tare Da Kone Motocinsu A Garin Kaduna

Image
Ankashe Mutane Tare Da Kone Motocinsu A Garin Kaduna Bayan asarar rayukan mutane 55, gwamnati ta saka dokar hana fita a kwaryar Kaduna

A yau Lahadi ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da sanarwar saka dokar ta baci tare da hana mutane fita na tsawon sa'o'i 24 a kwaryar birnin Kaduna da kewaye domin dakile yaduwar tarzomar da ta tashi a garin
A wata sanarwa da Samuel Aruwan, mai taimaka gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna a bangaren yada labarai, ya fitar, ya bayyana cewar dokar hana fitar za ta fara aiki nan take. Dokar ta bacin na zuwa ne kwanaki uku bayan barkewar rikici mai nasaba da addini a kasuwar Magani da ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane 55 da asarar dukiya mai tarin yawa. Da ranar yau, Lahadi, ne wani sabon rikicin ya nemi ya barke a garin Kaduna bayan bullar wata jita-jita da ta saka mutane cikin firgici da gudun neman mafaka. Kazalika akwai rahotanninn da suka bayyana cewar an kone motoci a kan titin Ahmadu Bello da kuma jin karar harbin bindiga a titin Jos.

Kalli Photunan] Yadda fitattun jarumai suka raya ranar samun yancin Nijeriya

Image
[Kalli Photunan] Yadda fitattun jarumai suka raya ranar samun yancin Nijeriya
; Jarumai kama daga Sani Danja, Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Hafsat Idris, Classiq, Nafisa Abdullahi, Rahama Sadau, Yakubu Muhammed zuwa Mansura Isa sun raya zagoyowar wannan rana.
Maryam Yahaya tayi adon taya Nijeriya murnar cika shekara 58 da samun yanci

Ranar litinin 1 ga watan Octoba al'ummar Nijeriya sun waye gari suna murnar zagayowar ranar samun yanci, suma jaruman arewa sun raya wannan ranar farin ciki.
Jaruman sun raya wannan ranar ta sakon da suka wallafa a shafukan su na kafafen sada zumunta.

Cikin su akwai mawaka da fitattun jaruman masana'antar kannywood.

Jarumai kama daga Sani Danja, Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Hafsat Idris, Classiq, Nafisa Abdullahi, Rahama Sadau, Yakubu Muhammed  zuwa Mansura Isa sun raya zagoyowar wannan rana.

Wasu da dama sun wallafa hotuna na musamman da suka dauka na taya murnar bikin cika shekara 58 sanye da riguna mai dauke da launin kasar tare da yin ado masu jan ha…