Oops! It appears that you have disabled your Javascript. In order for you to see this page as it is meant to appear, we ask that you please re-enable your Javascript!
News

Rikicin ‘yan Shi’a: ‘sun yi amai sun lashe’ kan harbin ‘yan Shi’a

Rundunar sojin Najeriya ta goge wani bidiyon na Shugaban Amurka Donald Trump wanda ta kafa hujja da shi wuri bude wa ‘yan Shi’a wuta.A cikin bidiyon, Shugaba Trump ya ce sojoji za su iya amfani da karfi kan baki ‘yan ci rani da ke jifansu da duwatsu.”Idan suka yi jifa da duwatsu… ku dauka sun yi da bindiga ne,” in ji Mista Trump a wani faifan bidiyo.Jami’an tsaron Najeriya sun ce mabiya Shi’a uku sun mutu a wani mummunan artabu tsakaninsu na tsawon kwanaki a Abuja.ko da yake mabiya Shia sun ce an kashe musu kusan mutum 50.Hujjar da sojin suka kafa da bidiyon Mr Trump ta jawo musu mummunar suka daga bangarori da dama na al’uma.Watakila hakan ne ya sa ranar Juma’a rundunar sojin ta goge sakon bidiyon ko da yake ba ta fadi dalilinta na daukar matakin ba.

Gabanin goge bidiyon, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta soki sojojin kasar da kashe ‘yan Shi’a, inda kuma ta ce zanga-zangar ‘yan Shi’ar ta lumana ce.

Sai dai mai magana da yawun sojojin kasar Burgediya Janar John Agim ya ce sun yi amfani da harsasai masu rai ne ga masu zanga-zanga saboda suna dauke da makamai.

Ya ce: “Wannan ne abin da Mista Trump yake magana a kai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker
%d bloggers like this: