Oops! It appears that you have disabled your Javascript. In order for you to see this page as it is meant to appear, we ask that you please re-enable your Javascript!
News

Subhanallah Gobara Ta hallaka Mutane Har 35 A Nigeria Hoto

Mutum 35 aka tabbatar da mutuwarsu a wata gobara da iskar gas ta haddasa a garin Lafiya na jihar Nassarawa, yayin da wasu daruruwa suka samu rauninka.

Rahotanni sun ce wata tankar dakon gas ce ta kama da wuta a wani gidan man Natson da ke kan babban titin da ya hada Abuja da Arewaci da kuma kudancin kasar.

Kuma wutar ba ta tsaya a anan kadai ba, domin ta kona motocin da ke ajiye a bakin hanya da kuma masu wucewa, da kuma kona shaguna da dama

Gobarar ta tayar da hankalin mazauna yankin da abin ya shafa.

Mutanen da gobarar ta rutsa dasu sun samu munanan kuna

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker
%d bloggers like this: