Oops! It appears that you have disabled your Javascript. In order for you to see this page as it is meant to appear, we ask that you please re-enable your Javascript!
News

Tashin hankali a Kaduna yayinda masu garkuwa suka kashe sarkin Adara 

An kashe Sarkin Adara – Agwom Adara – Maiwada Raphael Galadima wanda masu garkuwa suka sace a ranar Juma’ar da ya gabata, 19 ga watan Oktoba tare da matarsa. An tattaro cewa an kashe Galadima a ranar Alhamis, 25 ga watan Oktoba. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an tsinci gawar basaraken ne a safiyar ranar Juma’a, 26 ga watan Oktoba da safe kafin daga bisani aka kai shi asibitin St. Gerald Catholic Hospital da ke jihar Kaduna. Wani jami’in kungiyar Adara Development Association wanda ya ga gawar a asibitin yace an harbi marigayi Agom sau biyu

An kashe Sarkin Adara – Agwom Adara – Maiwada Raphael Galadima wanda masu garkuwa suka sace a ranar Juma’ar da ya gabata, 19 ga watan Oktoba tare da matarsa. An tattaro cewa an kashe Galadima a ranar Alhamis, 25 ga watan Oktoba. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an tsinci gawar basaraken ne a safiyar ranar Juma’a, 26 ga watan Oktoba da safe kafin daga bisani aka kai shi asibitin St. Gerald Catholic Hospital da ke jihar Kaduna. Wani jami’in kungiyar Adara Development Association wanda ya ga gawar a asibitin yace an harbi marigayi Agom sau biyu a kai Jami’in ya ce akwai harbin bindiga ta wajen kunnensa zuwa wuya.

A cewarsa masu garkuwan sun karbi wasu makudan kudade a matsayin kudin fansa kafin su kashe shi. A baya legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta sake mayar da dokar hana fita na sa’o’i 24 a birnin Kaduna da kewayenta, Kasuwan Magani, Kajuru, Kateri da kuma Kachia. Wannan doka zai fara aiki ne daga karfe 11 na safiyar yau Juma’a, 26 ga watan Okotoba har illa-ma-shaa’a.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close

Adblock Detected

Please consider supporting us by disabling your ad blocker
%d bloggers like this: